Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kaduna : muna garkame makaratun da suka ki yin bibiya da umarnin mu

Published

on

Maaikatar ilimin jahar Kaduna ta bibiyi wasu daga cikin makarantun kudin da ta samu labarin cewa basu bi umarnin da maaikatar ta bayar ba na cewa a garkame makarantun jahar daga ranar litinin 23 ga watan  Maris din nan har sai nan da kwana talatin.

Batun garkame makarantun dai ya biyo bayan bullar balahirar cutar nan ne na KORONA VIRUS (covid 19) a cewar sa kwamishinan ilimin jahar Shehu Muhammed Makarfi sun dauki matakin garkame makarantun ne dan takaita yaduwar cutar duk da ba a samu bullar cutar a jahar ba, a cewar sa matakan kariya ne kawai ake dauka.

A nata bayanin daraktar dake kula da ingancin makarantu a jahar Umma K. Ahmad wacce ita ce ta jagoranci tawaga dan tabbatar da makarantu sun bi dokar da aka basu tace basu kama Ko da makaranta guda daya na gudanar koyarwa ba.
“mun samu labarin cewa makarantu na ci gaba da karatu a makarantun su, sai dai kafin muzo sun kulle, dama kuma abunda muke so ke nan”

Daga karshe ta shawarci iyayen yara da su sanya ido akan yayan su yanda ya kamata musamman ma wajen killace yayan su a gida da kuma bin dokokin da jamian lafiya suka bayar da tabbatar da yaran sun bi dokar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!