Labarai
Kotu ta bayar da belin Nasir El-rufai

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya samu beli daga Kotun Tarayya.
A hukuncin da kotun ta yanke, an amince da bayar da belin ga El-Rufai bayan sauraron bukatar da lauyoyinsa suka gabatar, inda kotun ta ga ya dace a ba shi damar fita bisa wasu sharudda.
Sai dai har yanzu ba a bayyana cikakken bayani kan sharuɗɗan belin ba, yayin da ake sa ran zai ci gaba da fuskantar shari’ar da ake yi a kansa a gaban kotun.
You must be logged in to post a comment Login