Kaduna
Kaduna: Za a gurfanar da waɗanda suka kwashi kayan Corona a kotu

Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta cafke mutane 25 da ake zargi da hannu wajen wawashe kayan tallafin Corona a jihar.
Jami’in hulɗa da jama’a na ƴan sandan jihar ASP. Muhammad Jalige shi ne ya tabbatar da hakan ga wakilinmu Haruna Ibrahim Idris.
Cikin wadanda aka kama har da mace, kuma za a gurfanar da su a gaban kotu domin yanke musu hukunci a cewarsa.
You must be logged in to post a comment Login