Connect with us

Labarai

Siyasa ba da gaba ba: Mustapha Jarfa ya nemi gafarar Gawuna

Published

on

Ɗan siyasar nan Mustapha Jarfa ya nemi afuwar mataimakin gwamnan Kano kan wasu kalaman ɓatanci da yayi a kan sa.

A ranar 22 ga watan Disamba na shekarar 2018 ne Jarfa ya fitar da wani faifan bidiyo ta kafafen sada zumunta wanda ciki yayi kalaman ɓatanci ga mataimakin gwamnan Nasiru Yusuf Gawuna.

Kuma a watan Janairu na shekarar 2019 wata kotu a nan Kano ta yanke masa hukuncin ɗauri, wanda daga bisani kuma aka bada belinsa, sannan aka ci gaba da shari’a.

Lauyan mataimakin gwamnan Barista Aminu Abdullahi ya ce neman afuwan jarfar ya kawo karshen shari’ar tun da ya amince bisa radin kansa cewa yayi kuskure.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 334,910 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!