Kiwon Lafiya
Kamata ya yi ayi wa duk dan Najeriya gwajin ta’ammali da miyagun kwayoyi – Buba Marwa
Shugaban hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) Burgediya Janar Muhammad Buba Marwa mai ritaya, ya ce, ya kamata a rika yi wa kafatanin al’ummar Najeriya gwaji don ganin ko suna ta’ammali da miyagun kwayoyi ko akasin haka.
Ya ce hukumar ta bijiro da batun yin gwaji ga ‘yan siyasa, ma’aikata da kuma dalibai a baya-bayan nan ne da nufin taimaka wa wadanda aka samu sun yi dumu-dumu wajen ta’ammali da miyagun kwayoyi, don su daina dabi’ar.
Janar Buba Marwa mai ritaya wanda ya bayyana hakan lokacin da ya ke sanya hannu kan yarjejeniya da wani kamfani da zai yi kwangilar shigo da na’urar gwaje-gwajen kwayoyin, ya ce, yin gwaji ga kowa da kowa zai taimaka gaya wajen rage ta’ammali da miyagun kwayoyi a kasar nan.
Shugaban hukumar ta NDLEA ya kuma bayyana farin cikinsa da sanya hannu kan yarjejeniyar a wannan karon, wanda ya ce, tun a shekaru uku da suka gabata ne gwamnatin tarayya ta amince da sayo na’urar yin gwajin.
You must be logged in to post a comment Login