Kiwon Lafiya
Kamfanin NNPC ya ce ba shi da wani shirin gudanar da ritaya ga ma’aikatansa
Kamfanin mai na kasa (NNPC), ya ce ba ya da wani shiri na gudanar da ritaya ga ma’aikatan sa.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun kamfanin Ndu Ughamadu.
Sanarwar ta ce shugaban kamfanin na (NNPC) Maikanti Baru ne ya bayyana haka yayin wani taro jiya a Abuja.
Maikanti Baru ta cikin sanarwar dai ya bukaci ma’aikatan da su kwantar da hankulansu su ci gaba da aikinsu kamar yadda suka saba a ko da yaushe.
Ya ce ritaya da kamfanin yayi ga wasu daga cikin jami’an sa a baya-bayan nan, yana alaka ne da rashin kula da aiki