Kiwon Lafiya
Kamfanin NNPC ya ce ya biya fiye da naira biliyan na tallafin mai a shekara ta 2017
Kamfanin mai na kasa NNPC ya ce ya biya naira biliyan dari da arba’in da hudu da miliyan hamsin da uku wajen ba da tallafin mai a shekarar 2017 da ta gabata.
Hakan na kunshe ne ciki wani rahoton karshen shekara da kamfanin ya fitar wanda kididdiga ke nuna cewa a duk rana kamfanin ya kashe naira miliyan 366 wajen ba da tallafin mai.
Haka zalika rahoton ya kuma ce kudaden wani bangare ne na naira biliyan dari takwas da hamsin da bakwai da miliyan talatin da shida da kamfanin ya saka a asusun tarayya a shekarar ta 2017.
Kididdigar kudaden tallafin man ya nuna cewa a watannin Janairu da Fabrairu da Maris da Afrilu da Mayu da kuma Yuni, kamfanin na NNPC, ya biya naira biliyan 79 da miliyan 507.
Yayin da kuma a watannin Yuli zuwa Disamba kamfanin ya biya naira biliyan 65 da miliyan 22.