Labaran Kano
Kananan hukumomin da Korona tafi Kamari a Kano
Gwamnatin Kano ta bayyana cewa kashi 83 cikin 100 na cutar Corona ya fi shafar kananan hukumomi 10 na jihar.
Babban jami’in kwamitin kar ta kwana na kwamitin yaki da cutar Corona a jihar Kano Dr, Tijjani Hussain ne ya sanar da hakan a ya yin gabatar da rahoto kan cutar Korona a fadar gwamnatin jihar Kano.
Dr, Tijjani Hussain ya ce akasarin kananan hukumomin da suke cikin birnin Kano cutar ta COVID-19 ta fi shafa ya yin da sauran suka fito daga yankunan karkara.
A cewar shugaban yawan masu dauke da cutar ba zai rasa nasaba da yawan mutane dake zaune a cikin kananan hukumomin cikin birnin Kano ba, kasancewar hakan ya sanya cutar ta yi ta yaduwa
Ya ce daga cikin kananan hukumomin akwai Tarauni da Nasarawa da Fagge da Gwale da Dala da Birni da kewaye.
Sauran su ne Kumbotso da Ungogo da Wudil da kuma karamar hukumar Dambatta.
You must be logged in to post a comment Login