Labaran Kano
Kano: An zargi ‘yan sintiri da kisan kai
Runduna ‘yan sandan jihar Kano ta bayyana cewa ta kame wasu ‘yan sintiri da ake kira da Vigilante da ke unguwar Ja’en a yankin Sharada wadanda ake zargi da yiwa wani magidanci dukan da ya yi sanadiyyar rasuwarsa.
Kakakin rundunar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da kamen na su a tattaunawarsa da wakilin Freedom Radio Abba Isa Muhammad.
Rahotonnin sun bayyana cewa, marigayin mai suna malam Usman Mustapha Gwarzo ma’aikaci ne mai kula da injin bada fitilun kan titi.
A zantawar mai dakin marigayin Amina Musbahu da Freedom Radio, ta ce, ‘yan sintirin ne suka je da safe suke shaida mata cewa sun same shi ne a wurin injin tare da abokansa 2 inda suke tunanin ko sun je satar mai ne nan take suka fatattake su da gudu ba tare da sun san shi mai aiki ne a wurin ba.
Yana gudun ne sai ‘yan sintirin suka cimmasa inda suka lakada masa duka, kuma bayan kai shi asibiti ne daga bisani ya rasu yayin da suka je gidan shi don shaida mata yana sashen bada agajin gaggawa a kwance.
A zantawar Freedom Radio da shugaban kungiyar ta Vigilante Muhammad Kabir Alhaji, ta wayar tarho ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ya ce marigayin ya fada kwata ne kuma sun dauko shi suka kuma mika shi asibiti, don bashin agajin gaggawa.
Kakakin rundunar ‘yan sandan ya kuma bayyana cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano Ahmad Isiyaku, ya bada umarnin mayar da ‘yan sintirin zuwa shalkwatar rundunar da ke Bompai domin fadada bincike.