Labarai
Kano: Babu rahoton bullar cutar COVID-19 -Dr, Aminu Tsanyawa
Gwamnatin jihar Kano ta ce ya zuwa yanzu ba a samu bullar cutar Covid 19 wato Coronavirus anan Kano ba.
Kwamishinan lafiya na jihar Kano Dr Aminu Ibrahim Tsanyawa ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai da safiyar yau.
Ya ce gwamnatin jihar Kano ta na daukar tsauraran matakai domin ganin cutar ba ta yadu zuwa nan jihar Kano ba.
Dr Aminu Ibrahim Tsanyawa ya Kuma ce ya Kuma shawarci jama’a da su rika daukar matakan kariya musamman wajen wanke hannayensu akai akai.
Wakilin mu Abdullahi Isah ya ruwaito kwamishinan yada labarai na jihar Kano Kwamared Muhammed Garba wanda shi ma ya halarci wajen taron manema labaran da safiyar yau na cewa, maaikatar yada labarai ta jihar Kano za ta ci gaba da wayar da kan jama’a domin kare alummar jihar Kano daga cutar
You must be logged in to post a comment Login