Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kano bata dace da APC ba – Ra’ayin Bello Sharaɗa

Published

on

Daga Bello Muhammad Sharaɗa

A tarihi Kano gari ne na ilimi. Kano gari ne na addini. Kano gari ne na kasuwanci. Kano gari ne na sarauta. Kano gari ne ‘yanci da walwala da tarbiyya. Kano ana yi mata kirari da Tumbin Giwa, jallabar Hausa ko da me ka zo an fika. Limisliki alfun.

Ka auna tarihin Sarakunan Kano na Hausa da Sarakunan Kano na Fulani. Ka koma yadda Kano take bayan Turawan mulkin mallaka sun zo har suka ci mu da yaki a 1903 da lokacin da aka bamu ‘yancin kai a 1960, da sanda aka kirkiro jihar Kano a 1967.

Da zamanin soja na Audu Bako da Sani Bello da Ishaya Aboi Shekari kafin a baiwa farar hula mulki a jamhuriya ta biyu a shekarar 1979 da zamanin mulkin Rimi da Abdu Dawakin Tofa da Sabo Bakin Zuwo a tsakanin shekara biyar 1979-1984.

Da yanayin da gwamnonin sojoji suka yi mulki a shekara 15 tun daga watan Augusta 1985 har zuwa watan Mayu 1999, aka yi gwamna Hamza Abdullah da Idris Garba da Ahmad Daku da Ndatsu Ummaru da Kabiru Gaya da Abdullahi Wase da Dominic Oneya da Aminu Isa Kwantagora basu saba da tsarin Kano ba sai a shekara bakwai da take hannun Hadimu.

Abin da ya jawo haka, an kauce tsarin Kaka da kakanni na siyasar Kano da tsarinta da dabi’unta. Jihar Kano ta dada sukurkucewa ne a zamanin mulkin APC na Gandujiyya.

Duk girman Kano da daukakarta da yawan jama’a da Allah ya hore mata, mutum biyar ne kadai sai abin da suka shata, suka kitsa ko kana so ko baka so. Sun ce lokacinsu ne. Da sannu zasu tafi.

Labarai masu alaƙa:

APC Kano: Jam’iyyar APC ta kamo hanyar wargajewa

Ina nan a jam’iyyar APC – Murtala Sule Garo

Na farko gwamna Ganduje. Na biyu uwargidansa Farfesa Hafsat. Na uku Murtala Sule Garo. Na hudu Abdullahi Abbas. Na biyar Alasan Ado Doguwa. Mataimakin gwamna Ganduje sunansa ma Mota ba Fasinja saboda ba shi da wani tasiri, an ajiye shi safayar taya. Takarar gwamna da aka ba shi dole ce uwar naki. Shi kuma Usman Alhaji Sakataren gwamnati hoto ne.

A gefe guda kuma suka dan dosana shugaban majalisar jiha Rt Hon Chidari. Wanda duk bai gamsu ba ya tambayi Dr Baba Impossible.

Babu wani abu da za a yi sai da izinin wadannan mutanen. Rigimar G7 da kafuwar NNPP ita ce kadai ta rage kaifin Goggo da Dan Sarki da Alasan Doguwa.

Burin dan Sarki ya zama Sarki, burin Goggo kwamanda ya zama gwamna, burin Ganduje ya zama Sanata ko mataimakin shugaban kasa. Burin Alasan Ado Doguwa ya maye gurbin Femi Gbajabimilla.

Su biyar din nan kowa da bukatar da ta hada su.

Zaka gansu jumlatan, amma zuciyoyinsu daban-dabam. Dukkansu suna jifan juna. Murtala ya taba keta Alasan, ya taba cakume Abdullahi Abbas, a kwanan nan kuma Alasan Ado sai da ya mari Murtala a gaban Gawuna kuma a cikin gidansa.

Alasan zai iya zagin kowa da sunan siyasa. Hatta Ahmed Aruwa sai da Alasan ya hankade shi a gaban mahaifiyarsa. A gaban Abdullahi Adamu shugaban jam’iyya na kasa na APC da gwamna Ganduje ya hayayyako wa Sardaunan Kano, har suka yi cacar baki da Aliko Dan Shuaiba, aka shiga tsakani.

Yan wannan guruf din sune suka tsangwami Barau, an kai matsayin da Sanata Barau bai isa ya zo taro ba a Kano sai dai ya yi harkarsa a Abuja. Kwanan nan Sanata Barau ya baiwa Ganduje kyautar miliyan 150.

Abin da ya nace APC ba ta dace da Kano ba, a wadannan shekarun ne gwamna Ganduje ya kalli manyan masu daraja ya keta musu alfarma, sannan ya kirasu da Dattawan Wukari.

A wannan lokacin ne gwamna ya dauki aikin da aka zabe shi domin ya aiwatar amma ya danka shi a hannun uwargidansa, har kuma ta nada wanda zai gaje shi.

An kai matsayin da komai ba a yinsa daidai a Kano a mulkin Ganduje. In kuma ka tanka sai a daureka. Ko a saka wasu karnuka su yi tayi maka haushi. GA Kano garin kasuwanci an yanka kasuwa ko ina ba tsari.

Kullum a cikin rigimar fili. Kano garin Sarauta, ita kanta masarautar an yi mata filla-filla, Alasan Ado Doguwa ma Sardaunan kasar Rano ne, da rawaninsa ma ya kwankwashi bakin Murtala. Kano garin malanta, Council of Ulama sai da aka yi mata kishiya, hatta halifancin Tijjaniya sai da aka kutsa ga na Sarki ga na gwamna.

Siyasa kuma ba a zancenta, Rarara ya taba zambo da tsulan biri aka yi masa tafi. Ya yi habaici da duna aka yi masa dariya. Ya buga misali da hankaka ana shirin kulle shi.

Babu wani lamarin APC da ake yi cikin adalci. Kowa kuka yake yi. Ga shi kansa Mai gidan APC na kasa babu wani abin alheri mai girma da aka yi wa jama’ar Kano a saboda kauna da biyayya da goyon baya da suke yi masa tsawon shekara 18.
APC bata dace Kano ba. A 2023 Sai an canza da kuri’armu cikin yardar Allah

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!