Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kano: Dabi’ar zuwa makaranta a makare ya zama ruwan dare ga dalibai

Published

on

Dabi’ar nan ta zuwa makaranta a makare da wasu dalibai musamman na firamare da sakandare ke yi a nan Kano, har yanzu ana fama da ita, don kuwa har kimanin karfe 10 na safe  mafi yawan lokuta akan ga wasu dalibai kan hanya maimakon kasancewarsu cikin ajjuwansu, domin daukar darasi , tun da kuwa ana shiga aji ne da 8:30 na safe ne.

Ga dukkan alamu zuwa makaranta a makare da daliban ke yi na neman zamewa abin yau da kullum kasancewar kusan yanzu a iya cewa zuwa a makaren ba ya tayarwa da daliban hankali, watakila ko don ba a daukar matakin da ya kamata a kansu ne.

A bincikin da Freedom Rediyo ta gudanar ya bayyana  cewa akwai daliban da ke zuwa makaranta a makare wanda ya zame musu dabi’a ta yadda wasu ma sai lokacin da ake komawa tara ne suke yiwa makarantar shigar farko.

Wasu dalibai da muka yi kacibis da su da misalin karfe goma na safe a unguwar Rijiyar-Zaki sun bayyana mana dalilan da ya sanya suke makara zuwa makaranta.

Asibitin kashi na Dala ya fadakar da dalibai illar gobara

Ahmed Musa zai dauki nauyin karatun dalibai 100 a jami’a

Abun takaici ne mawadata basa tallafawa dalibai-Dr, Nafi’u Dan-nono

Inda suke cewa  dalilin da yasa suke makara bai wuce idan sunje makaranta basa samun malam su ba, a cewar su malaman nasu su ma a makare suke shiga makarantar domin koya musu darasu.

 

Babbar sakatariya a ma’aikatar illimi ta jihar Kano, Hajiya Lauratu Diso ta ce dalillan da ke sanyawa yara zuwa makaranta a makare shi ne rashin fitowa a akan lokaci ko kuma su tsaya a wani wajen, inda ta ke cewa sakacin iyaye ne a matsayin su na daya daga cikin dalillan faruwar hakan.

Hajiya Lauratu Ado Diso ta kara da cewar,  kamata  yayi iyaye su sa ido sosai akan yaran su ko suna zuwa makaranta akan lokaci kuma akasin haka.

Kazalika Babbar sakatariyta  ta ce  gwamnati ta shirya wani tsari da zai kai ga kara sanya ido sosai kan dalibai masu irin wannan dabi’a ta zuwa makaranta a makare da kuma yaa zame musu jiki.

Dalibai

Wakiliyar mu Hafsat Abdullahi Danladi ta ce Hajiya Lauratu ta kuma kara da cewa suma malamai ya kamata su sa ido sosai akan yara

Babbar sakatariyar ta ja hankali iyaye da su rinka sanya ido sosai kan ‘ya’yansu a kowane lokaci don tallafawa gwamnati ta wannan fuska.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!