Labarai
Kano: Hisbah ta yi sulhu da masu gidajen kallo da wuraren shaƙatawa
Hukumar Hisbah ta yi sulhu da masu gidajen kallo da wuraren shaƙatawa da masu ɗakunan taro na jihar Kano.
A Talatar nan ne Hisbah ta gana da shugabannin ƙungiyoyin su domin tattauna yadda za a samu daidaito a tsakani wajen gudanar da ayyukansu.
Babban Kwamandan Hisbah Malam Haruna Ibn Sina ya ce, suna fatan ganin masu gidajen kallo da wuraren shaƙatawa su sanya musulunci a cikin ayyukansu.
A cewarsa, ba gaskiya ba ne labarin da ake yaɗawa na cewa Hisbah za ta rufe gidan kallo ko wurin shaƙatawa domin ba ta da wannan hurumin.
Karin labarai:
Black Friday: An samu saɓani tsakanin Hisbah da majalisar malamai a Kano
Tallafin Corona: An dakatar da kwamandan Hisbah na Dala
Kwamandan ya ƙara da cewa, za su yi haɗin gwiwa da shugabannin ƙungiyoyin ta yadda za su riƙa aiki tare domin tabbatar da ba a keta dokokin musulunci ba.
Manyan abubuwan da Hisbah ta ja hankalin ƙungiyoyin sun haɗa da, sanya idanu kan ƙananan yara da ke zuwa wuraren, da kuma masu shaye-shayen miyagun ƙwayoyi.
Sai kuma batun zuwan ƴan mata wuraren shaƙatawa barkatai.
Da yake mayar da jawabi a madadin ƙungiyoyin Murtala Tijjani ya yaba wa hukumar ta Hisbah kan yadda ta nuna kulawa a gare su har ta gayyace su domin tattaunawa.
You must be logged in to post a comment Login