Labarai
Kano: Hukumar Hisbah ta kama shahararren ɗan TikTok Ukasha UK

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama wani shahararren ɗan TikTok mai suna Ukasha Yahaya, wanda aka fi sani da UK International, mai shekaru 27.
Rahotanni sun ce an kama matashin ne bisa zargin wallafa wasu bidiyoyi a kafar TikTok da ke nuna shi tare da mata cikin yanayin da hukumar ta ce bai dace da tarbiyya da al’adun al’umma ba.
Mataimakin Babban Kwamandan Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Dakta Mujahid Aminuddeen, ne ya tabbatar da kamen matashin a wani sokon murya da aikowa Freedom Radio.
You must be logged in to post a comment Login