Connect with us

Labarai

Yan Majalisar wakilai sun kada kuri’ar neman kawo karshen yaƙin Amurka da Iran

Published

on

Yan Majalisar wakilan Amurka sun kada kuri’ar neman kawo karshen yaƙin da ƙasar ke yi da Iran, ta hanyar amincewa da wani kudurin da zai takaita ikon Shugaba Donald Trump na ci gaba da kai hare-haren soji ba tare da amincewar Majalisa ba.

Kuri’ar da aka kada ranar Talata ta samu kuri’u 220 da 204, inda ‘yan jam’iyyar Republican bakwai suka goyi bayan kudurin, Wannan dai shi ne karo na uku da Majalisar ke daukar irin wannan mataki, bayan makamantan kudurori a watan Yuni da Yuli.

Sai dai har yanzu ba a san ko Majalisar Dattawa za ta amince da kudurin ba. A baya ma Majalisar Dattawa ta amince da kudurin kawo karshen rikicin, amma ‘yan Republican sun sauya matsayinsu washegari, bayan da Shugaba Trump ya soki kudurin.

Trump ya kare matakin sojin Amurka a Iran, yana mai cewa yakin ya raunana karfin sojin kasar. Wannan dai ya zo ne duk da cewa a lokacin yakin neman zabensa na wa’adi na biyu, ya yi alkawarin ba zai jefa Amurka cikin yake-yake na kasashen waje ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!