Labaran Kano
Kano: INEC ta raba kayayyakin zaben ranar Asabar
Yanzu haka hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa dake nan Kano INEC ta fara raba kayayyakin aikin zabe zuwa kananan hukumomi tara na Kano da kotu ta bada umarnin a sake gudanar da zabe a wasu wurare.
Kamar yadda aka tsara dai za a gudanar da zaben ne a jibi Asabar 25 ga wannan wat ana janairu da muke ciki.
Tuna dai shirye-shirye suka yi nisa na rabon kayayyakin zaben, wanda kuma wakilan jam’iyyu daban-daban suka halarci shalkwatar hukumar domin shaida yadda rabon kayan ke gudana.
Jami’an tsaro ne dai za su yiwa kayayyakin domin ganin an kai su wuraren cikin kwanciyar hankali, da kuma tabbatarda cewa an kai kayayyakin zaben guraren da suka dace domin gudanarda zaben.
Wakilinmu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa da ya kasance a a shalkwatar hukumar ta INEC lokacin rabon kayan ya ruwaito cewa tun da sanyin safiyar yau ne Alhamis 23 ga Janairun 2020 ne jami’an tsaro suka yiwa shalkwatar kawanya domin tabbatar da tsaro musamman wajen ganin an gudanar da rabon kayayyakin cikin kwanciyar hankali da lumana.