Connect with us

Labarai

Kano: Majalisa ta amince da sabbin dokoki 2

Published

on

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da kudirin dokar Tsare-tsaren Birane da Kula da Ci gaban Gine-gine ta bana, wanda ya soke dokar da ta kafa Hukumar tsara Birane da Raya Kasa ta Jihar Kano, wato KNUPDA.

 

An zartar da kudirin ne bayan karatu na biyu da na uku a zaman majalisar da aka gudanar a jiya Talata, karkashin jagorancin shugabanta Majalisar,  Jibril Ismail Falgore.

 

Da ya ke ƙarin bayani bayan zaman,  shugaban masu rinjaye a majalisar, kuma wakilin Dala, Hon. Lawan Hussaini, ya ce sabuwar dokar ta kafa Hukumar Kula da Yankin Birnin Kano (KAMA) da kuma Hukumar Kula da Tsare-tsare da Gina Muhalli ta Kano (KADCA), wadanda za su gudanar da ayyukansu karkashin Ma’aikatar Filaye da tsarin Birane.

 

Haka kuma yayin zaman, shugaban majalisar, Jibril Ismail Falgore, ya kaddamar da kwamitin wucin gadi da zai hada gwiwa da Sakataren Gwamnatin Kano domin daidaita ayyukan Ma’aikatar Noma da Ma’aikatar Raya Kiwon Dabbobi.

 

Ana sa ran kwamitin zai sa ido kan mika dukkan harkokin kiwon dabbobi, kiwon kifi da sauran ayyukan da suka shafi kiwo daga Ma’aikatar Noma zuwa Ma’aikatar Raya Kiwon Dabbobi, kamar yadda Majalisar ta amince.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!