Labarai
Kano: Yan sanda sun kama wanda ake zargi da yin amfani da kayan sojoji tare da kai wa yan bindiga harsasai

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce ta kama wani mutum da ake zargi da amfani da kayan sojoji na bogi tare da kai wa ‘yan bindiga harsasai a karamar Hukumar Bichi.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, a kuma rabawa manema labarai.
Sanarwar ta bayyana cewa an kama Mohammed Isah Haruna mai shekara 28 ne bayan bayanan sirri da aka samu cewa wani mutum sanye da kayan soja yana yawo a kauyen Rimaye da ke karamar hukumar Bichi.
Sanarwar ta ce bayan bincike, jami’an rundunar tare da haɗin gwiwar al’ummar yankin sun kama shi tare da kwato harsasai, kayan sojoji, hulunan sojoji, katin shaidar aikin soja na bogi da sauran kayayyaki.
Sanarwar ta kara da cewa wanda ake zargin ya amsa cewa ya je yankin ne domin kai harsasan da sauran kayayyakin da aka kwato ga ‘yan bindigar da ke cikin daji.
Rundunar ta ce, tana ci gaba da bincike domin kamo sauran wadanda ake zargi da hannu a lamarin kafin gurfanar da shi a kotu.
You must be logged in to post a comment Login