Labaran Wasanni
Kano Pillars ta dakatar da daukar sabon mai horar wa
Kwana 1 bayan sanar da sunayen mutum 6 da take shirin tantance su ta kuma dauki 1 cikin su, a matsayin sabon mai horas war ta kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta sanar da dakatar da shirin.
A ranar Laraba mai zuwa 1 ga watan Satumba kungiyar dai ta sanar a matsayin ranar da za ta tantance masu horarwawar, kafin daga bisani ta sauya aniyar hakan.
Kano Pillars ta fitar da sunayan masu horarwa 6 da za ta tantance
Rahotanni sun tabbatar da cewar , kungiyar ba ta bayyana dalilan dakatar da tantancewar ba, kamar yadda mai magana da yawun ta Rilwanu Idris Malikawa Garu, ya tabbatar, da dakatarwar.
“An dakatar da tantancewar da kuma shirin daukar, za’a kuma a sake sabon tsari na daukar mai horar war” a cewar Malikawa.
A ranar Lahadi 29 ga Agusta 2021, kungiyar ta Pillars , ta sanar da sunayen mutum shida , da tace za’a tantance su a Talata don samar da sabon mai jagorantar tawagar a Kakar wasannin shekara mai kamawa ta 2021/22.
You must be logged in to post a comment Login