Labaran Wasanni
Kano Pillars ta fitar da sunayan masu horarwa 6 da za ta tantance
Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, ta fitar da sunayan masu horarwa 6 dake neman aikin horar da ‘yan wasan kungiyar.
Hakan na cikin wata sanarwa da Mai magana da yawun ta Lurwanu Idris Malikawa Garu, ya fitar a yau Lahadi 29 ga Agustan shekarar 2021.
Sanarwa ta ce an zabo mutanen daga cikin masu neman aikin horar da ‘yan wasan kungiyar 25 da suka mika takardun bukatar su.
Abin da ya sa muka raba gari da mai horaswarmu – Kano Pillars
Kazalika sanarwar ta ce mutane 6 da aka fitar da sunayan na su anasaran za su zo Kano a ranar Talata 31 ga watan na Agusta, inda za su gabata a gaban kwamatin tantancewar a ranar Laraba 01 ga watan Satumba mai kamawa.
Sanarwa ta ce masu nemai aikin da aka fitar da sunayan nasu sun hadar da Busari Hakeem Ishola da Henry Makinwa da Salisu Yusuf da Erol Akay da Emanuel Amunike sai kuma Usman Shareef Abdallah.
Malikawa ya ce za’a sanar da sunan Wanda ya samu nasara da an gama tantancewar
Idan za’a iya tunawa a makon da ya gabata ne kungiyar ta Kano Pillars ta sanar da cewa, sai mai horarwar dake da lasisin hukumar kwallon kafa ta Africa CAF ne zai ci gaba da jagorantar kungiyar.
You must be logged in to post a comment Login