Labaran Wasanni
Kano Pillars ta nada Salisu Yusuf a matsayin mai horarwar ta
Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta nada Salisu Yusuf a matsayin sabon mai horar da ita.
Nadin Salisu Yusuf zai sa ya jagoranci kungiyar a kakar wasannin shekarar 2021/22 a gasar Firimiya ta Najeriya NPFL.
Salisu ya dawo kungiyar ne bayan shekaru 12 da ya kasance a baya tare da tawagar.
Tin da fari dai ya kasance a kungiyar da akewa take da Sai Masu Gida a kakar wasannin 2007/2008 da a lokacin ya jagoranci Pillars lashe gasar firimiya ta farko.
Haka zalika ya sake dawowa a karo na biyu a shekarar 2010, inda ya taimaki kungiyar samun damar buga gasar cin kofin nahiyar afrika ta CAF Champions League.
Da yake jawabi a mamadin gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje mataimakin gwamna Nasir Yusuf Gawuna cewa yayi yana fatan nadin da kungiyar ta yi mishi zai kawo mata ci gaba da kuma fatan samun nasarori.
“Salisu D-Black mutum ne me kwarewa, wanda ya taba jagorantar kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles,”
“Da muke saran ya san ciki da waje na dukkanin al’amuran wasanni, wanda muke da kwarin gwiwa da kuma tabbaci akan zai bamu gudun mawa yadda ya kamata,” a cewar Gwamna Ganduje.
Ana saran dai fara sabuwar kakar wasanni ta shekarar 2021/2022 a karshen wata mai kamawa da kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars na da cikin kungiyoyi 20 da zasu fafata a gasar ta NFPL.
You must be logged in to post a comment Login