Labarai
Kano: Yan sanda sun kama matasa 2 bisa zargin yunkurin sace Dagaci

Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta kama wasu matasa biyu bisa zargin yunkurin sace wani Dagacin kauye a Ƙaramar Hukumar Gezawa.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, CSP Abdullahi Haruna, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.
Sanarwar ta ce Dagacin mai suna Malam Idris ya kai korafi ga ‘yan sanda a ranar 26 ga Oktoba, 2026, inda ya bayyana cewa wani mutum da ba a san ko wanene ba ya kira shi ta waya yana yi masa barazanar sace shi.
Haka kuma, sanarwar ta kara da cewa, bayan samun rahoton, jami’an ’yan sanda sun gudanar da bincike, wanda ya kai ga kama waɗanda ake zargin, Aliyu Naziru Garba mai shekara 20 da Bashir Alhasan mai shekara 20.
You must be logged in to post a comment Login