Labarai
Kwmatin yaƙi da fadan daba da miyagun ƙwayoyi ya kamo Malam Keya a birnin Fatakwal

Kwmatin yaƙi da fadan daba da miyagun ƙwayoyi ta jihar kano, ta kama wani matashi mai suna Ishaq Lawan Ibrahim, wanda aka fi sani da Malam Keya, mai shekaru ashirin da bakwai, a birnin Fatakwal na jihar Rivers.
Wannan na cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar inda Shugaban hukumar, Muhuyi Magaji Rimin Gado, ya tabbatar da kama shi din.
Ta cikin sanarwar Rimin Gado ya ce, ana zargin Malam Keya, wanda ɗan unguwar Yelwa ne da ke ƙaramar hukumar Dala a Kano, da jagorantar tare da ɗaukar nauyin faɗan daba da ya addabi wasu sassan jihar, musamman ƙaramar hukumar Dala.
Sanarwa da hukumar ta fitar a yau Alhamis, ta kara da cewa, wanda ake zargin ya tsere daga nan Kano bayan tsananta ayyukan tsaro a wuraren da ake samun rikicin daba a wancan lokaci kuma tuni aka dawo da shi nan Jihar Kano.
Sanarwar ta ce jami’an hukumar, bisa sahihan bayanan sirri, sun bi sawun wanda ake zargin har zuwa Fatakwal, inda suka cafke shi a wani samame da shugaban ayyukan hukumar, CSP Bashir Gwadabe, ya jagoranta.
Hukumar ta ce wanda ake zargin yana tsare kuma za a ci gaba da gudanar da bincike a kansa, kafin gurfanar da shi a gaban kotu bayan kammala binciken.
You must be logged in to post a comment Login