Labarai
FRSC ta gargaɗi direbobi kan illolin gudu yayin da ake tafka ruwa

Hukumar Kiyaye Afkuwar Haɗura ta Najeriya FRSC ta gargaɗi direbobi da sauran masu amfani da hanya kan haɗarin yin gudu a tuƙi yayin da ake tafka ruwan sama, tare da buƙatar su ɗauki matakan kariya domin kauce wa haɗurra.
Hakan na kunshe cikin sanarwar da Jami’in Wayar da Kan Jama’a na Hukumar FRSC, Osondu Ohaeri, ya fitar.
A cikin sanarwar Shugaban Hukumar, Shehu Mohammed, ya bayyana cewa yawan ruwan sama kan rage gani ga direbobi tare da sa hanyoyi su yi santsi, lamarin da ke ƙara haɗarin afkuwar haɗura.
Shugaban ya buƙaci direbobi su tabbatar da cewa gilashin motarsu, fitilu da na’urar goge gilashi suna aiki yadda ya kamata kafin su fara tafiya.
Haka kuma, ya shawarci direbobi su rage gudu da zarar an fara ruwan sama, su tabbatar tayoyin motocinsu na da kyau kuma suna riƙe hanya yadda ya kamata domin rage haɗarin zamewa ko ƙwacewar abin hawan su.
Shugaban hukumar ya kuma umarci kwamandojin FRSC a faɗin Najeriya da su ƙara wayar da kan jama’a, kula da zirga-zirga da kuma tabbatar da ana duba ingancin na’urorin goge gilashin motoci a wannan lokaci na damina.
You must be logged in to post a comment Login