Connect with us

Labarai

Sojoji sun kama wanda ake zargin jagoran ’yan ta’adda ne a Kaduna

Published

on

Dakarun Operation Fansan Yamma sun kama wani da ake zargin jagoran ’yan ta’adda da wasu mutane biyu da ake zargin abokan hulɗarsa ne a Ƙaramar Hukumar Kubau ta Jihar Kaduna.

Rundunar ta ce a wani samame na daban a Ƙaramar Hukumar Igabi, an kama wata mata mai shekaru 50 tana jigilar harsasai 300 da ake zargin za a kai wa ’yan ta’adda a Birnin Gwari.

Sojojin sun kuma kama wani da ake zargin mai samar wa ’yan ta’adda kayan aiki ne, tare da ƙwato na’urorin sadarwa guda huɗu da ake kyautata zaton suna da alaƙa da ayyukan ta’addanci.

An tsare waɗanda ake zargin tare da kayan da aka ƙwato domin ci gaba da bincike da gano sauran mutanen da ke cikin wannan hanyar sadarwa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!