Labarai
Kano: yan ta’adda sun hallaka mutane 2 a harin da suka kai Tsanyawa

Rahotanni daga tsohon garin Kamaye da ke karamar hukumar Tsanyawa a jihar kano, sun bayyana yadda wasu gungun ‘yan ta’adda suka kai wani mummunan hari a garin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 2 tare da jikkata wasu da dama
Majiyar mu da ta nemi a sakaye sunan ta , ta tabbatar mana da faruwar lamarin da misalin karfe 6 na yammacin jiya Litinin.
Bayan samun bayai ne kuma jam’ian soji da ke kusa da kauyen suka garzaya tare da fatattakar yan ta’addan.
Ya zuwa wannan lokaci dai, babu wata sanarwa ta hukumomin da abin ya shafa kan lamarin.
Karamar hukumar tsanyawa na daya daga cikin wuraren da ke fama da hare-haren ‘yan ta’adda a jihar Kano, lamarin da gwamnatin jihar ta sha nanata cewar zata dauki matakin dakile matsalar.
You must be logged in to post a comment Login