Labaran Kano
Kano zata hada kafada da kasashen duniya a bangaren ilimi –Ganduje
Gwamnatin jihar Kano, ta sha alwashin bunkasa harkokin ilimi dana lafiya, don yin kafadu da takwarorin su na kasashen duniya, kasancewar su su ne kashin bayan cigaban dukkan wata al’umma, jiha ko kasashe.
Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana haka a yayin wani taron daya gudana a gidan gwamnati da manyan sakatarorin da manyan jami’an gwamnati don dubawa da kare kasafin kudin shekara ta dubu biyu da ashirin, na ma’aikatu daban daban na jiha.
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya ce duk da cewar wasu bangarori na da matukar muhimmanci musamman ma bagaren Noma da kuma harkokin tsaro, gwamnatin sa zata bada fifiko ne wajen Ilimi, da harkar lafiya don haka ta fito da tsarin yin ilimi kyauta kuma wajibi.
Tun da fari da yake jawabi shugaban ma’aikata na jihar Kano, Dr Kabir Shehu yace sun zo ne don gabatarwa tare da kare kasafin kudaden shekarar ta 2020, na ma’aikatu daban -daban dake jihar nan.
Wakilinmu Aminu Halilu Tudunwada, ya ruwaito mana cewa, gwamna Ganduje ya yi alkawarin gabatar da yan majalisar zartawar wa wato kwamishinoni nan ba da dadewa, don su gudanar da ayyukan da kasafin kudin ya kunsa na ma’aikatun su daban -daban don cigaban jihar da kuma al’ummar ta.
RUBUTU MASU ALAKA:
Yaran Kano 9: Ganduje ya kafa kwamitin bincike na musamman