Addini
Kano9: Ina rokon mahukunta su magance satar yara -Sheikh Kariballah Kabara
Shugaban darikar Kadiriyya na Afrika Sheikh Dr. Karibullah Nasiru Kabara ya yi kira ga Shugabanni da su mayar da hankali wajen magance matsalolin sace-sacen yara da matsalolin fashi da makami maimakon su zauna suna suna abubuwan da basu kamata ba wanda hakan wajibi ne a kansu.
Yayin wata tattaunawa da Freedom Radiyo tayi da Sheikh Kariballah Nasiru Kabara a yayin da yake shirin fitowa domin tafiya filin Maukibi da mabiya darikar kadiriyya ke gudanarwa a yau, ya nemi shugabanni dasu mayar da hankali wajan magance matsalolin rashin tsaro dake addabar fadin kasar nan.
Labarai masu alaka:
Gwamnatin tarayya ta bada hutun Maulidi
Wadansu magidanta sun karbi Musulunci a garin Sumaila
Sheikh karibullahi yayi kira ga mahukunta kan idan ankama masu laifi yana da kayau a rinka gurfanar dasu a gaban shari’a domin yanke musu hukunci wanda hakan zai taimaka gaya wajen rage aikata laifuka musamman ta bangaren shaye-shaye da sara suka.
A yau Asabar ne ake gudanar da maukibin Kadiriyya karo na 69 wanda mabiya darikar ke yi a duk shekara da nufin tunawa da ranar haihuwar Sidi Abdulkadir Jilani.
Maukibin wanda Sheikh Muhammd Nasiru Kabara ya assasa lokacin yana raye, ya fara shi ne da mutane 40, a yanzu kuma daruruwa ne ke halartar taron daga jihohin kasar nan da wasu daga cikin kasashen ketare.
Labarai masu alaka:
Ilimantar da mata kamar ilimantar da al’umma ne- wani malamin addini
An horar da daliban Aminu Kano yadda ake gudanar da aikin Hajji