Labaran Kano
Karin farashin wuta da man fetur ya nuna Najeriya na cikin halin ni’yasu – Masani
Masanin tattalin Arzikin na Jami’ar Bayero dake nan Kano, Farfesa Ibrahim Garba Sheka ya ce karin farashin man fetur da wutar lantarki da gwamnati ta yi ya nuna karar tattalin arzikin kasar nan na cikin halin
Farfesa Ibrahim Garba Sheka ya ce cire tallafin da gwamnati ta yi daga fetur da kuma siyar da wutar lantarki, shi ya haddasawa hau-hawar farashin kayayyakin masarufi da ake fama dashi a yanzu.
Don haka nan gaba ma idan gangar mai ta ci gaba da hau-hauwa a kasuwar duniya, to babu shakka farashin man fetur zai kara yin tsadar da sai mutane sunyi mamaki.
Ibrahim Garba Sheka ya kara da cewar tattalin arzikin kasar nan ya ta’allaka ne lacokan a kan fetir wanda kuma a yanzu gwamnatin tarayya ta janye tallafin da ta ke bayarwa, wanda da shi ne ake samun saukin al’amuran rayuwa.
Farfesa Garba Sheka ya kuma ce, rashin mayar da hankali wajen alkinta kayayyakin da kasar nan ke sarrafawa da kuma sauyin kudaden waje sune suka sabbaba karyewar darajar kudin kasar nan a idon duniya.
Farfesan ya jadda da cewa, bude boda shine mafita mafi sauki ga talaka zai samu sassauci ga al’amuran kasar nan.
You must be logged in to post a comment Login