Coronavirus
Karin mutum 2 masu Corona sun mutu a Kano

Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta ce a yanzu haka karin mutum biyu daga cikin masu dauke da cutar a jihar Kano sun rasu.
Cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na Twitter tace yanzu haka adadin wadanda suka rasa ransu sanadiyyar cutar sun kai mutum uku.
As at 12:15pm 27th April 2020, @KanostateNg records an additional 2 deaths of #COVID19#StayHomeSaveLives #StaySafeNigeria pic.twitter.com/VcPeqJEmuJ
— Kano State Ministry of Health (@KNSMOH) April 27, 2020
Izuwa yanzu dai jimillar wadanda suka kamu da cutar a Kano sun kai mutum 77 a sanarwar ma’aikatar lafiyar.
Yanzu haka dai cibiyar gwajin cutar Corona dake Kano ta shafe tsawon kwanaki a rufe sakamakon rashin kayan aiki.
You must be logged in to post a comment Login