Labarai
Karuwar jama’a shike kawo matsalar ruwan sha a Kano
Hukumar samar da ruwan sha ta jihar Kano tace matsalolin ruwan sha da ake fuskanta a yanzu a jihar Kano nada nasaba da karuwar jama’a a birnin na Kano.
Daraktan mulki na Hukumar Injiniya Musbahu Nasir ne ya bayyana haka a cikin shirin Duniyar mu a yau na nan Freedom Radio.
Injiniya Musbahu yace kwararowar wasu al’ummar zuwa jihar Kano na da nasaba da karancin ruwan
Mazauna Tokarawa sun yi kururuwar neman dauki
Al’ummar Dakata sun koka akan ginin shaguna bisa magudanar ruwa
Shi kuwa Injiniya Magaji Hussain cewa yayi har yanzu akwai bukatar karin wasu sababbin matatun ruwa a Kano kasancewar yawan mutane a Kano yana karuwa wanda hakan yasa jama’a ke cigaba da kara tsananin bukatar ruwan a yanzu.
A nasa bangaren shugaban hukumar samar da ruwan sha ta Jihar Kano yace matsalar ruwan sha da ake faman cece kuce akai a Kano musamman a kwaryar birnin na da alaka da rashin hakuri da kuma yadda wasu ke Siyasantar da al’amarin.
Bakin sunyi kira ga al’ummar Kano dasu kara hakuri domin kuwa nan da shekaru shida masu zuwa matsalar rashin ruwan sha a Kano za tazo karshe.
You must be logged in to post a comment Login