Labarai
Karuwar rashin aikin yi barazana ce ga ƙasa – Chris Ngige
Ministan kwadago da samar da aikin yi Dakta Chris Ngige ya ce, karuwar rashin aikin yi Barazana ce ga ƙasa .
Ministan ya bayyana hakan lokacin da ya halarci taron tattaunawa kan tattalin arziki wanda ma’aikatar ayyuka na musamman ta shirya a Abuja.
Ngige ya ce, rashin ilimi babbar barazana ce da zata kara haifar da matsaloli a kasar nan, inda yayi gargadin cewa matukar aka gaza magance ta, to kuwa kasar za ta shiga cikin wani yanayi.
Har ma ya ce, rashin aikin yi ga matasa lamari ne da zai kara haifar da matsalolin tsaro da kuma matsin tattalin arziki.
You must be logged in to post a comment Login