Labarai
Kasafin kudin badi na Kano ya tsallake karatu na biyu
Majalisar dokokin jihar Kano ta bai wa kwamitinta da ke kula da kasafin kudi wa’adin daga nan zuwa ranar goma sha bakwai ga watan gobe na Nuwamba domin ya gabatar da rahotonsa kan kunshin kasafin kudin badi da gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya gabatar a ranar Alhamis na makon jiya.
Idan za a iya tunawa a ranar Alhamis da ta gabata ne gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya gabatar da kunshin kasafin kudin ga majalisar dokokin jihar Kano.
Tun da farko dai majalisar ta bukaci ma’aikatu da hukumomin gwamnati na jihar ta Kano da su zo gaban kwamitocinta daban-daban wadanda suke kula da ma’aikatun domin kare kunshin kasafin kudinsu.
Kai tsaye: Ganduje ya kammala gabatar da kasafin kudin 2020
Majalisar dattijai zata mikawa shugaba Buhari kunshin kasafin bana a Juma’ar nan
Abunda ya kamata ku sani kan kasafin kudin badi
Majalisar ta kuma dage cigaba da zamanta har zuwa ranar goma sha shida ga watan gobe na Disamba domin dawowa ta ci gaba da tattana batun daftarin kasafin kudin.
Haka zalika shugaban majalisar Abdulaziz Garba Gafasa ya ce bayan dawowa daga hutun majalisar za ta sanar da ranar da za a gudanar da taron jin ra’ayin jama’a kan kunshin kasafin kudin.