Labaran Wasanni
Kasar masar ta nada tsohon mai horar da ‘yan wasan Real-Madrid a matsayin sabon jagoran ta
Kasar masar ta bayyana tsohon mai horas da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real-Madrid Carlos Queiroz a matsayin mai horar da ‘yan wasan kasar.
Hakan ya biyo bayan sallamar mai horas da ‘yan wasan na Masar Hossam El-Badry da kasar ta yi sakamakon Kunnan Doki da kasar ta yi a wasan neman tikitin buga gasar cin kofin Duniya da za’a gudanar a kasar Qatar a shekarar 2022.
Qatar 2022: Kasar Masar ta sallami mai horar da ‘yan wasan ta
Kazalika kasar ta bayyana Diaa El-Sayed, a matsayin mataimakin sa sannan tsohon mai tsaron ragar kasar Essam El-Hadary a matsayin jami’in kungiyar
Carlos Queiroz mai shekaru 68 ya jagoranci kungiyar kwallon kafa ta kasar Portugal zuwa gasar cin kofin Duniya a shekarar 2010 ya kuma horar da ‘yan wasan kasar Iran a shekarar 2014 zuwa 2018.
You must be logged in to post a comment Login