Ƙetare
Kasar Rasha ta gargadi Ecowas kan juyin mulkin Nijar
Ƙasar Rasha ta gargaɗi ƙungiyar Ecowas game da ɗaukar matakin soji da ta ce za ta yi kan sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar.
Tana mai cewa matakin ka iya haifar da rikicin da zai daɗe ba a ga ƙarshensa ba.
Cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Rasha ta fitar a jiya Juma’a, ta gargaɗi ƙasashen yammacin Afirka da kada su aika sojoji zuwa Nijar.
Yanzu haka dai Manyan hafsoshin tsaron ƙasashen Ecowas na shirin wata ganawa a yau Asabar domin tsara yadda za a shirya dakarun sojin.
Tuni dai shugaban ƙasar Ivory Coast, Alassane Ouattara, ya ce ƙasarsa za ta tura sojoji kimanin 1,000 waɗanda za su bi sahun sauran dakarun ko-ta-kwana da za su zauna cikin shirin don turawa Nijar din.
Ƙasashen Amurka da Faransa da kuma Tarayyar Turai tuni suka goyi bayan matakin da ƙungiyar Ecowas ta ɗauka, domin mayar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Mohamed Bazoum kan karagar mulki.
.
You must be logged in to post a comment Login