Kiwon Lafiya
Kasar Saudiya ta tsayar da 3 ga Maris shekara ta 2019 a matsayin ranar rufe karbar adadin alhazai
Kasar Saudi Arabiya ta tsayar da ranar 3 ga watan Maris din shekarar da muke ciki a matsayin ranar da zata rufe karbar takardar bukatar yawan alhazan da za’a yi jigilar su daga kamfanonin jiragen sama.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugabar sashen yada labarai na hukumar kula da aikin hajji ta kasa NAHCON Fatima Sanda Usara.
Sanarwar ta kara da cewa hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kasar saudiyya ce ta bayyana hakan, a yayin da wakilan ta suka gudanar da taro da wakilan hukumar kula da aikin hajji ta kasa kan yadda aikin hajjin bana zai gudana a birnin Jidda da ke Saudiyya.
Ta cikin sanarwar dai ta bayyana cewa shugaban hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta kasar Saudiyyan Mr.Samir Shami na kira ga masu kamfanonin jiragen sama da su mika takardun bukatar su akan lokaci.
Da ya ke bayani a madadin hukumar NAHCON Kwamishinan kula da ayyukan na hukumar Alhaji Abdullahi Saleh ya bayyana wasu hanyoyi da za’a bi na magance irin matsalolin da aka samu a hajjin shekarar bara.