Tsaro
Kasar Turkiyya za ta girke sansanin sojojin ta a Najeriya

Najeriya da Turkiyya sun amince da kafa babbar cibiyar horon soji a Najeriya, a wani ɓangare na haɗin gwiwar tsaro tsakanin ƙasashen biyu.
An cimma yarjejeniyar ce lokacin wata tattaunawar diplomasiyya tsakanin ministocin tsaron ƙasashen biyu a a gefen taron diplomasiyya na 2026.
A ƙarƙashin yarjejeniyar dakarun tsaron Najeriya za su riƙa samun horo a fannoni daban-daban na yaƙi da matsalar tsaro kamar ta’addanci da tattatara bayanan sirri da amfani da jirage marasa matuƙa da cire abubuwan fashewa da aka dasa, da kuma atisayen ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD.
Najeriya ta jima tana neman haɗin kai da taimakon manyan ƙasashen waje wajen yaƙi da ayyukan ƙungiyoyin ƴanbindiga masu ɗauke da makamai a ƙasar.
A watan Fabrairu ne Amurka ta tura dakaru 200 zuwa Najeriya, domin ayyukan horas da sojojin Najeriya da taimaka musu da bayanan sirri.
You must be logged in to post a comment Login