Tsaro
Rundunar Sojin Najeriyar ta lalata maboyar ‘yan bindiga a jihar Borno

Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta bayyana cewa hare-haren jiragen yaki da ta kai sun lalata maboyar ‘yan ta’adda a yankin Southern Tumbuns da ke Jihar Borno.
Rundunar ta ce an gudanar da farmakin ne ranar Juma’a 24-04-2026 da misalin karfe 6:50 na yamma bayan samun sahihan bayanan sirri kan ‘yan tada kayar baya.
Mai magana da yawun rundunar, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya ce jiragen yaki sun fara sintiri inda suka gano wasu ‘yan ta’adda suna bi ta hanyoyin boye zuwa wasu gine-gine da ke karkashin bishiyoyi masu yawa. Bayan tabbatar da su, sai aka kai musu hari da makamai daga sama.
NAF ta ce farmakin ya yi nasara domin an lalata maboyar ‘yan ta’addan, lamarin da zai rage musu karfi a yankin. Rundunar ta kuma jaddada cewa za ta ci gaba da matsa wa ‘yan ta’adda lamba domin kare kasa da al’umma baki daya.
You must be logged in to post a comment Login