Connect with us

Labarai

Shufaba Tinubu ya buƙaci AU ta ɗauki mataki kan hare-haren ƙyamar baƙi a Afirka ta Kudu

Published

on

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci kungiyar Tarayyar Afirka AU ta ɗauki mataki kan abin da ya kira hare-haren ƙyamar baƙi da ake kai wa ‘yan Afirka da sauran ƙasashen duniya a Afirka ta Kudu.

Shugaban ya bayyana hakan ne a wani taron musamman na Tarayyar Afirka da aka gudanar a Luanda, babban birnin Angola, inda Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya wakilce shi.

Tinubu ya ce irin waɗannan hare-hare na barazana ga haɗin kan ƙasashen Afirka da zaman lafiya, don haka ya nemi a sanya batun cikin ajandar taron ƙoli na Tarayyar Afirka da za a gudanar a watan Janairun shekara mai zuwa, domin a tattauna tare da ɗaukar matakin da ya dace.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!