Labarai
Kaso 54.6 na yaran Kano ƴan ƙasa da shekaru 5 aka yi wa rijistar haihuwa- UNICEF
Asusun tallafa wa ƙananan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF, ya ce, kawo yanzu kimanin kaso Hamsin da huɗu da ɗigo shida cikin ɗari na yaran da suke kasa da shekaru biyar aka yi wa rijistar haihuwa a jihar kano duk da irin alfanun da yin rijistar ke da shi.
Shugaban ofishin UNICEF na Kano Rah ma Rihood Mohammed ne ya bayyana hakan, yayin taron tattaunawa da manema labarai kan wayar da kai bisa sabunta tsarin yin rijistar haihuwar ta manhaja watau “DIGITAL”.
Ya ce, akwai buƙatar kafafen yada labarai su kara zaburar da al’umma don ganin kowanne yaro ya mallaki rijistar haihuwa.
“La’akari da mahimmancin da mallakar rijistar haihuwa ke da shi, Domin haka hakki ne akan kowanne iyaye su tabbatar sun sama wa yaran su rijistar haihuwa saboda rayuwarsu ta gaba”
A nasa ɓangaren, Daraktan hukumar kidaya ta Kasa NPC, Alhaji Isma’il ya bayyana cewa, a watan Oktoban da ya gabata hukumar su ta samu damar yi wa yara daga shekaru biyar zuwa ranar haihuwa 225,408,163 a fadin Nijeriya.
Ya ƙara da cewa, hakan ya samo asali ne bisa yadda asusun na UNICEF ya samar Da wadatattun kayan aiki a dukkan kananan hukumomi.
You must be logged in to post a comment Login