Ƙetare
Ketare:Fasinjoji 5 sun mutu a kogin atlantika bayan batan jirgin ruwa mai nitsewa
Fasinjoji biyar dake cikin jirgin ruwa mai nutsewa daya bata a karkashin teku sun mutu, a cewar wani jami’i a cikin dakarun tsaron gabar tekun Amurka.
Kamfanin dake lura da sufurin jirgin mai suna Titan ya ce mutanen biyar masu tafiye tafiyen, bincike ne na hakika wadanda suka yi tarayya akan kudirin kwakuduba.
Mutanen dake cikin jirgin sun hadar da Stockton Rush, babban jami’in kamfanin OceanGate mai shekaru 61 da kuma wani dan kasuwar Burtaniya dan asalin Pakistan Shahzada Dawood da dan sa Sulaiman.
Haka zalika akwai wani dan kasuwar Burtaniya Hamish Harding dan shekara 58, sai kuma cikon na biyar din Paul Henry tsohon sojan Ninkayar Faransa dan shekara 77 da yayi fice wajen tafiye-tafiyen binciken kasa.
Dakarun tsaron gabar Tekun sun ce an gano wani fili mai cike da tarkacen jirgin Titanic, wadda a yammacin jiya Alhamis yayin wani taron manema labarai Rear Admiral John Mauger na rundunar tsaron gabar Tekun Amurka yace an yi imani tarkacen suna da kama da sassan jirgin dake tafiya karkashin tekun.
Rahoton: Mukhtar Abdullahi Birnin Kudu
You must be logged in to post a comment Login