Connect with us

Labarai

Kisan Ƴar Aiki: Yadda zaman kotu ke kasancewa kai tsaye

Published

on

Ku ci gaba da bibiya ana sabunta wannan shafi da sabbin bayanai kan yadda zaman kotun ke kasancewa.
Nasir Salisu Zango

Kotu ta hana belin wadda ake zargi sannan ta ɗaga shari'ar zuwa ranar 16 ga watan Fabrairun da muke ciki domin ci gaba da shari'ar.

Basheer Sharfadi

Lauyanta yana ci gaba da roƙon kotun a bada belinta saboda tana fama da rashin lafiyar sanadiyyar ɓari da ta yi.

Sai dai lauyar Gwamnati ta ce, a gidan gyaran hali ma za a ci gaba da kula da lafiyarta.

Lauyoyin ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗanadam da daban-daban dana ƙungiyar mata lauyoyi ne suka yi cikar kwari a kotun domin sanya idanu kan shari'ar.

Basheer Sharfadi

An gurfanar da Fatima Hamza a gaban Kotun Majistiri mai lamba 8 bisa zargin ta da kisan kai.

Bayan karanto mata tuhumar wadda ake zargi ta musanta.

Lauyan da ke kare ta ya gabatarwa da Kotu takarda don neman belinta kasancewar bata da lafiya.

Sai dai lauyar Gwamnati ta yi suka kan ɓuƙatar ta sa.

Yanzu haka ana ta musayar yawu kan wannan batu.

Wakilin Freedom Radio da ke kotu Aminu Abdu Baka Noma ya rawaito cewa, Fatima ta bayyana a gaban cikin yana yin rashin lafiya.

Ya ce, da ƙyar ta ke tafiya, kuma ba ta iya tsayawa sai kujera aka bata ta zauna.

Fatiman tana sanye da Atamfa da Hijabi Yalo sannan tana riƙe da jaririya.

Ku ci gaba da bibiya muna sabinta wannan shafi da sabbin bayanai kan yadda daman kotun ke kasancewa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv

Now Streaming

Archives