Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Ko hukuncin Kotun Koli ya kawo karshen Siyasar Kwankwasiya a Kano?

Published

on

Daga Abdullahi Isah.

A jiya litinin Ashirin 20 ga wannan wata da muke ciki na Janairu Kotun Kolin kasar nan ta kawo karshen jayayya da ke tsakanin mabiya darikar Kwankwasiya da karkashin jagorancin tsohon gwamnan jihar Kano, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso da takwarorinsu na bangaren gwamnati ‘yan Gandujiyya a jagorancin gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje, sakamakon watsi da Kotun ta yi da bukatun da Dantakarar jam’iyyar PDP Injiniya Abba Kabir Yusuf ya gabatar gabanta wanda ya kalubalanci nasarar da gwamna Ganduje ya samu.

Kotun dai ta ki amincewa da bukatar PDP da Dantakarar ta Abba Kabir Yusuf na neman korar gwamnan na Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje daga mukaminsa.

Masu lura da lamuran yau da kullum da masu sharhin siyasar jihar ta Kano kawunan su ya rabu gida biyu kan wannan lamari, yayin da wasu ke ganin cewa wannan hukuncin ya kawo karshen siyasar Kwankwasiya a jihar Kano, wasu ko gani su ke har yanzu akwai sauran rina a kaba musamman idan aka yi la’akari da irin karfin da darikar Kwankwasiya ta yi a jihar ta Kano.

Masu ikirarin cewa siyasar Kwankwasiya ta zama tarihi bayan wannan hukuncin na Kotun Koli suna cewa, kasancewar tsohon gwamnan na Kano a yanzu babu wani mukamin siyasa da ya ke rike da shi kuma kusan duk mutanen sa babu wani da ya ke rike da wani mukami mai gwabi, hakan zai yi matukar wahala ya iya lallaba darikar Kwankwasiya musamman idan aka yi la’akari da cewa dama jam’iyyar PDP a jihar Kano cike take da rikice rikice.

Rikicin Gwamnatin Kano da Masarauta: Siyasa ko cigaba?

Shekarar 2023: Mecece makomar Takai a siyasar Jahar Kano?

Haka zalika sun ma ce burin Kwankwaso na neman takarar shugaban cin kasar nan zai samu koma baya sakamakon cewa babu isassun kudade da za’a rike ‘ya’yan jamiyya kasancewar kowa ya sani a kasar nan siyasa ba ta dorewa in ba kudi, wannan ne ma ya sa masu adawa da tsohon gwamnan su ka yi zargin cewa ai burinshi na tabbatar da Abba ya zama gwamnan Kano shine domin ya samu dama ya mayar da jihar Kano Saniyar tatsarsa, inda duk wata za a ware wani kaso mai tsoka ga kwamitin yakin neman zaben gwamnan kamar yadda aka yi da kudaden kananan hukumomi a shekarar dubu biyu da goma sha biyar 2015.

Bugu da kari akwai zargin cewa jam’iyyar a wannan karon fa ba za ta kyale tsohon gwamnan yayi abinda ya ga dama a jihar Kano ba, musamman ganin cewa babu isassun kudade a hannun shi saboda haka za ta so bai wa dukkannin ‘ya’yan jamiyyar dama a rika damawa dasu wanda hakan bako shakka zai janyo koma baya ga ci gaba da dorewar darikar Kwankwasiya.

A bangare guda wasu na ganin cewa zai yi matukar wuya tsohon gwamnan na Kano Kuma tsohon Sanata mai wakiltar mazabar Kano ta tsakiya ya ci gaba da kasancewa a jam’iyyar PDP musamman ganin cewa a yanzu babu gwamnati ko goyon bayan gwamnati a tattare dashi adon haka zai gwammace ya koma jam’iyya mai mulki ko ba komai watakila hakan za ta sanya Darikar Kwankwasiya ta ci gaba da numfasawa.

Sai dai ana ganin cewa akwai dama ta zama mataimakin shugaban kasa. Sai dai masu wannan ra’ayi ba su yi karin haske kan ko tsohon gwamnan zai yi sulhu da tsohon abokin tafiyar sa a siyasa ba ne wato gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ko Kuma kowa zai ci gashin kansa ne wato a yi zaman ‘yan marina.

Idan muka koma ga masu ikirarin cewa Darikar Kwankwasiya za ta ci gaba da bunkasa, suna da ra’ayin cewa ai ko da a zaben shekarar dubu biyu da goma sha daya 2011, lokacin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya sake dawowa gwamnan Kano a karo na biyu ba ya rike da mukami kuma hasalima bai samu goyon bayan gwamnati a sama ba a lokacin duk kuwa da cewa suna jami’yya daya.

Sun Kuma nanata cewa daga lokacin da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bar mukamin gwamnan Kano zuwa yanzu, Darikar Kwankwasiya kara bunkasa ta ke a kullu yaumin ,hujjarsu kuwa ita ce a lokacin da yake gwamna iyakarta Kano kafin ya nuna sha’awarsa na takarar shugaban kasa a shekarar dubu biyu da goma sha biyar (2015), wanda yanzu kuma Darikar ta Kwankwasiya ta karade jihohin Arewacin kasar nan har ma ta leka wasu jihohin da ke Kudanci, kamar yadda suka yi ikirari.

Sannan akwai masu ganin cewa ma saboda irin dumbin magoya baya da Darikar Kwankwasiya ke da ita zai sa Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya zamo wata bazawara mai farin jini tsakanin masu neman darewa karagar mulkin kasar nan a shekarar dubu biyu da ashirin da uku 2023, wanda zasu nemi hadin kansa domin ya kasance mataimakin shugaban kasa, wanda wannan Kuma ka iya faruwa a jam’iyyar sa ce ta PDP ko Kuma a jamiyya mai mulki a yanzu wato APC.

Magana ta gaskiya koma me zai kasance nan gaba Allah ne kawai masani amma ga duk wanda zai yi nazari irin ta siyasa zai yadda dani cewa wannan hukuncin na Kotun Koli zai yi tasiri wajen ci gaba da kasancewar Darikar Kwankwasiya ko kuma gaza dorewarta.

Rubutu daga Abdullahi Isa

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!