Labaran Wasanni
Ko Real Madrid za ta iya daukan Laliga?
A makon daya gabata ne kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta samu nasarar doke kungiyar kwallon kafa ta Barcelona da ci 2-0 a wasan hamayya na kasar Espaniya, wanda ake wa lakabi da El-clasico.
Nasarar da Real Madrid ta samu kan Barcelona da ci 2-0 ya bawa Real Madrid damar darewa saman teburin La ligar.
Sai dai a wasan wannan mako 27, Ungulu ta koma gidanta na tsamiya bayan da Madrid din ta yi rashin nasara a hannun Real Betis da ci 2-1, yayin da Barcelona ta doke Real Sociedad da ci 1-0 wanda hakan ya bawa Barcelona damar komawa matakin farko da maki 58, Madrid ke biye mata da maki 56.
LABARAI MASU ALAKA
Shin ko Atletico Madrid za ta samu nasara kan Liverpool?
Madrid na fuskantar barazanar ficewa daga Champions League
Hukuncin kotu ba zai hana mu lallasa Madrid ba – Guardiola
A wasanni hudu da Real Madrid ta buga a kwanakin nan nasara daya ta samu tak wanda haka ba karamin koma baya bane ga kungiyar.
Levente 1 Real Madrid 0
Manchester City 2 Real Madrid 1 (Gasar cin kofin zakarun nahiyar turai)
Real Madrid 2 Barcelona 0
Real Betis 2 Real Madrid 1
Tun a kakar wasanni ta shekarar 2016-2017 Madrid bata kara lashe gasar ta La Liga ba, duk da cewa cikin wannan shekaru ta lashe gasar cin kofin zakarun nahiyar turai har sau uku a jere.
Magoya bayan kungiyar ta madrid na ganin cewa wannan rashin nasara da kungiyar ke samu na da alaka da rashin tsayayyen dan wasan gaba mai zura kwallo, kasancewar har yanzu kungiyar ta kasa samun dan wasan da zai maye gurbin, jagoranta a baya Cristiano Ronaldo wanda ya koma kungiyar kwallon kafa ta Junventus da ke kasar Italiya.
You must be logged in to post a comment Login