Labarai
Ko SWAT za ta sauya zani daga SARS?
A yau Litinin ne za a fara horas da jami’an sabuwar rundunar ƴan sanda ta SWAT da zata maye gurbin rundunar SARS da aka soke.
Rundunar ƴan sanda dai ta ce, jami’an da aka zaɓa waɗanda za su kasance cikin sabuwar rundunar matasa ne masu jini a jika kuma dukkansu sun shafe aƙalla shekara bakwai suna aikin ɗan sanda.
Sannan jami’an ba su da wani tabo ko kuma tarihi na laifi da suka aikata a baya, ba a kuma taɓa samunsu da laifin take haƙƙin bil adama ba ko kuma saɓa ƙa’idar amfani da makami.
Za dai a soma horas da ‘yan sandan ne a kwalejojin horas da ‘yan sanda na Ila Oragun, da ke jihar Osun da kuma kwalejin horas da ‘yan sanda ta jihar Nasarawa.
Labarai masu alaka:
ENDSARS: An yiwa EFCC kutse a shafukansu
EndSARS : Ya yi hanzari kirkiro SWAT – Kungiyar Gwamnoni
To sai dai masana tsaro na cewa da sauran aiki a gaban rundunar ƴan sanda matuƙar ba ta nazarci sake inganta ayyukan jami’anta ba maimakon sabuntawa, a cewar mai sharhi kan tsaro Malam Mustapha Isyaku da ke digirinsa na uku kan tsaro a makarantar sojoji ta NDA da ke Kaduna.
“Ni ina ganin abin da ya fi mahimmanci ba wai yau a ce an soke SARS sannan ayi hanzari a kirkiri SWAT ba, saboda babu wani dan Najeriya da ya ke ganin su SWAT ba za su yi abinda su SARS su ka yi ba” a cewarsa.
Ya kara da cewa “Ina ganin abin da ya fi mahimmanci shi ne a mayar da hankali wajen inganta gabaki daya tsarin rundunar ‘yan sanda, ya kasance kafin ma a dauki mutum ‘dan sanda an tantanceshi, ya kuma wuce duk wasu ka’idoji da horo da ya kamata a ce ya samu”
Ya ci gaba da cewa “Sannan akwai bukatar ci gaba da horas da su lokaci bayan lokaci, sannan akwai bukatar samar musu da kayayyakin aiki na zamani, sannan a koyar dasu gyara alaka tsakaninsu da al’umma, idan ba a yi haka ba babu wani sauyi da za a samu”.
You must be logged in to post a comment Login