Connect with us

Labarai

Za mu yanke hukunci kan makomar yan siyasar da aka cire su daga jerin yan takarar gwamna- INEC

Published

on

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, INEC, ta ce za ta yanke hukunci kan makomar tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Isa Pantami, Aminu Gwarzo, Ladi Adebutu da sauran ’yan siyasar da aka cire sunayensu daga jerin sunayen ’yan takarar zaɓen gwamnonin jihohi da za a gudanar ranar shida ga watan Fabrairun shekarar dubu biyu da ashirin da bakwai.

Kwamishinan INEC na ƙasa, Mohammed Haruna, ne ya bayyana hakan ga jaridar Punch a jiya, inda ya ce za a tattauna batun a taron hukumar na yau Alhamis.

 

Pantami na neman kujerar gwamnan jihar Gombe, yayin da Aminu Gwarzo ke takarar gwamnan Kano a ƙarƙashin jam’iyyar NDC, Ita kuwa Ladi Adebutu ta jam’iyyar PDP na neman kujerar gwamnan Ogun, yayin da Danjuma

 

Laah ke takarar gwamnan Kaduna a ƙarƙashin jam’iyyar NDC.

 

An cire sunayen ’yan takarar daga jerin da INEC ta wallafa ranar goma ga watan Oktoba. Haka kuma, hukumar ta cire ’yan takarar gwamna na jam’iyyun SDP, NNPP, Action Alliance da Accord a jihar Bauchi, waɗanda suka haɗa da Abdullahi Yakubu, Musa Zubairu, Ahmed Shuaibu da Mohammed Aminu, bi da bi.

 

Matakin ya jawo zanga-zanga da kuma ɗaukar matakan shari’a daga ’yan takarar da abin ya shafa da jam’iyyunsu, yayin da ake jiran matakin da hukumar za ta ɗauka kan lamarin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!