Labarai
Ma’aikata na ci gaba da fuskantar matsin tattalin arziki duk da ƙarin albashi- NLC

Kungiyar ƙwadago ta Kasa NLC ta yi gargaɗin cewa ma’aikata na ci gaba da fuskantar matsin tattalin arziki duk da ƙarin mafi ƙarancin albashi zuwa Naira dubu 70.
Kungiyar ta kuma jaddada cewa wa’adin makonni biyu da ta bai wa Gwamnatin Tarayya kan tsadar man fetur da sabon tattaunawar albashi yana nan daram.
Shugaban NLC, na kasa Joe Ajaero, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Abuja.
Ya kuma soki yadda ake aiwatar da yarjejeniyar sabon mafi ƙarancin albashin shekarar 2024, tare da buƙatar ɗaukar matakan gaggawa domin rage tsadar rayuwa.
Ajaero ya ce rage ƙarfin sayen kayayyaki da ma’aikata ke fuskanta na ƙara ta’azzara, don haka ya buƙaci gwamnati ta ɗauki matakan sauƙaƙa farashin man fetur tare da sake buɗe tattaunawar albashi.
Ya kuma yi kira ga gwamnati da ta magance matsalolin ma’aikata tun kafin lamarin ya kai ga shiga yajin aiki ko zanga-zanga.
You must be logged in to post a comment Login