Labaran Kano
Kotu ta aikewa Baban Chinedu sammaci kan zargin Afakallah
Kotun shari’ar musulunci dake unguwar Hausawar gidan Zoo a nan Kano ta aike da sammaci ga fitaccen jarumin fina-finan Hausa Haruna Yusuf, da aka fi sani da Baban Chinedu.
Kotun ta sanya ranar daya ga watan Afrilu mai zuwa domin sauraron karar da shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano Isma’il Na’abba Afakallahu ya shigar da Baban Chinedu, bisa zargin bata masa suna.
Kotun ta bukaci Baban Chinedu da ya bayyana a gabanta a ranar daya ga watan Afrilun domin fara sauraron karar.
Labarai masu alaka.
Ban baiwa Madam Korede mukami ba -Tambuwal
Addu’o’I sun fara nasara a Kannywood
Cikin takardar sammacin da aka aikewa da Baban Chinedu ta tabbatar dacewa in har bai halarci kotun ba, kuma an tabbatar ya samu wannan sammaci kotun zata yanke hukunci koda baya nan.
Kwanakin baya ne Baban Chinedu ya zargi shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano Isma’il Na’abba Afakallahu, da cewa ya yi sama da fadi da kudaden siyan kayan aure da gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bayar domin sayawa iyalan marigayi Rabilu Musa Dan Ibro.
You must be logged in to post a comment Login