Connect with us

Nishadi

Ban baiwa Madam Korede mukami ba -Tambuwal

Published

on

Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal,  ya karyata labarin da ake yadawa a kafafan sada zumunta na cewa ya nada fitacciyar jarumar barkwancin nan dake jihar Kaduna wato Maryam Aliyu Obaje wadda aka fi sani da Madam Korede,  mukami.

Cikin wata sanarwa da mai baiwa gwamnan jihar Sokoto shawara kan kafafan yada labarai Muhammad Bello, ya fitar a ranar Alhamis ya ce wannan labarin  kanzon kurege ne.

A yanzu haka gwamna Tambuwal yana jihar Delta domin gabatar da wasu ayyuka na musamman  don haka jama’a suyi watsi da wannan labari a cewar Muhammad Bello.

Labarai masu alaka.

APC zata daukaka kara kan shari’ar zaben gwamnan Sokoto

Buhari zai yi titi daga Sokoto zuwa Nijar

Tun da farko dai Madam Korede,  ce ta wallafa hoton ta da wani zane da akayi mata na taya ta murnar a matsayin sabuwar mai baiwa gwamnan jihar Sokoto shawara kan sabbin kafafan yada labarai, wanda daga baya  ta cire hoton da ta wallafa.

Freedom Radio tayi kokarin jin ta bakin jarumar amma hakan ta ya ci tura.

A tuntubar da Freedom Radio ta yi wa  matashin da ya yiwa Madam Korede zanen da ta wallafa a shafin ta,  ya tabbatar da cewa ita ce ta umarce  shi, ya yi mata wannan zanen.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!