Connect with us

Labarai

kotu ta bada umarnin tsare shugaban jam’iyyar ADC

Published

on

Wata kotun majistare da ke Birnin Kebbi, ta bayar da umarnin a tsare shugaban wani ɓangare na jam’iyyar ADC, Sufyanu Bala, bisa zarginsa da raina umarnin kotu kan takaddamar shugabancin jamiyyar.

 

Kotun ta ce za a ci gaba da tsare shi har zuwa lokacin sauraron bukatarsa ta neman beli.

 

Lauyan masu ƙara ya bayyana cewa matakin ya zama dole domin tabbatar da mutunta doka, ya na mai zargin Sufyanu Bala, da karya umarnin kotu.

 

Sai dai lauyan wanda ake ƙara ya musanta hurumin kotun majistare ɗin kan shari’ar, ya na cewa batun ya na gaban babbar kotu.

 

A nasa ɓangaren, Sufyanu Bala, ya zargi gwamnatin jihar da hannu a rikicin domin kawo cikas ga jam’iyyar.

 

Rikicin ya daɗe ya na faruwa a jam’iyyar ADC a Kebbi, inda ɓangarori daban-daban ke ikirarin shugabanci, lamarin da ke jefa shakku kan haɗin kan jam’iyyar gabanin zaɓukan shkarkar 2027.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!